Sunday, January 5
Shadow

‘Yanbindiga sun kai hari kasuwar Shinkafi tare da sace gomman mutane

Al’ummar garin shinkafin jihar Zamfara sun ce ‘yanta’adda sun kai wani hari kasuwar garin inda suka tafi da gwammon mutane tare da jikkata wasu.

Mazauna yankin sun ce ‘yanbindigar sun kai harin ne ana tsaka da cin kasuwar Shinkafin da ranar yau Alhamis.

Sai dai har kawo yanzu rundunar ‘yansandan jihar ta Zamfara ba ta ce komai kan harin.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da gawurtaccen ɗanbindingar nan da ke cin karensa babu babbaka a jihar Zamfara, Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan al’umma.

A makon da ya gabata ne dai sojoji suka kama wani makusancin ɗanbindigar al’amarin da ya ce ya fusata shi kuma zai ɗauki fansa.

Karanta Wannan  ZABEN 2027: Ba Muśĺim-Mùšĺìm Bà, Ko Mùmìñi-Mùmìñi Ne Ba Za Mu Zaba Ba, Inji Wani Fusataccen Ĺimàmi, Malam Abubakar Mai Imani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *