
Yansanda sun cafke wasu matasa da su ka tare kan titi, daidai shatale-talen gidan gwamnatin Kano su na yin bidiyo din barkwanci don samun “trending”.
Kakakin rundunar ƴansanda ta jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya baiyana hakan a shafin sa na Facebook.