
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta soke dakatarwar da majalisar Dattijai tawa sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Kotun tace a gaggauta dawo da sanata Natasha Akpoti bakin aikinta.
Mai shari’a, Justice Binta Fatima Nyako, ce ta yanke wannan hukunci inda tace dakatar da Sanata Natasha Akpoti ya dakile aikinta na wakiltar mutanenta.
Majalisar Dattijai dai ta dakatar da sanata Natasha Akpoti ne bayan da ta zargi kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio da nemanta da lalata.