Wednesday, January 15
Shadow

Yanzu-Yanzu: NLC zata ci gaba da yajin aiki gobe bayan zaman sulhu da Gwamnati ya gaza cimma matsaya

Rahoton da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC zata ci gaba da yajin aikin da ta dauri aniya gobe, Litinin bayan zaman sulhu da gwamnati ya ci tura.

A yau lahadi ne dai aka zauna tsakanin wakilan gwamnatin tarayya daga majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dan cimma matsaya kan mafi karancin Albashi, saidai an kare zaman ba tare da cimma matsaya ba.

Da misalin karfe 5:50 PM ne dai aka fara zaman inda aka kareshi da misalin karfe 8:45 PM.

Kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio bayan taron, ya gayawa manema labarai cewa gwamnati ta roki kungiyoyin kwadagon kan su janye yajin aikin nasu amma suka kiya.

Karanta Wannan  An Gudanar Da Addu'ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

Akpabio yace idan aka yi yajin aiki, abubuwa da yawa hadda asibitoci a kasarnan zasu tsaya cik.

Duk da haka dai ya sake rokon kungiyoyin kwadagon da su sake duba wannan matsaya tasu ta dagewa sai sun je yajin aikin.

Wakilin TUC, Festus Osifo ya bayyana cewa zasu yi yajin aikin har zuwa kamin su tattauna da membobinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *