A rahoton farko an ji cewa:
Tsananin zafi a hajjin bana alhazai 900 ne suka rasu!
Kamfanin dillancin labarai na AFP bayan tattara bayanai daga ofisoshin jakadancin ƙasashe na cewa aƙalla alhazai 922 ne suka mutu yayin aikin Hajjin, akasari saboda tsananin zafi da aka yi fama da shi. Lokacin Hajji a kasar Saudia. 2024
Alkaluman sun tabbatar da cewa Aƙalla ‘yan ƙasar Masar 1,400 ne aka ba da rahoton sun ɓace cikinsu har da 600 da suka mutu, kamar yadda wasu jami’an difilomasiyya suka shaida wa AFP.
Saidai sabon rahoton daga AFP ya tabbatar da cewa yawan alhazan da suka mutu sun kai 1081.