
Matashiya ‘yar kimanin shekaru 16 wadda ke ajin SS2 a makarantar Sakandare ta yi garkuwa da kanta inda ta nemi a biya kudin fansa Naira Miliyan 2.
Lamarin ya faru ne a Abakaliki, Jihar Ebonyi.
Matashiyar ta kira dan uwanta inda ta sanar dashi cewa an yi garkuwa da ita.
Wani dake da alaka da iyayenta ne ya taimaka mata wajan shirya wannan lamarin.
Kakakin ‘Yansandan jihar, Joshua Ukandu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama wadanda ake zargi kuma sa’a tabbatar an hukuntasu.