Sunday, January 26
Shadow

Yarbawa sunce basu yadda da kotunan shari’ar musulunci a jihohinsu ba

Kungiyoyin dake fafutukar kafa kasar Yarbawa sun bayyana rashin amincewa da bullar kotunan shari’ar Musulunci a jihohinsu.

Jihar Ekiti itace ta baya-bayannan da aka samu bullar kotun shari’ar Musulunci wadda har alkalai 3 Imam Abdullahi Abdul-Mutolib, Imam Abdulraheem Junaid-Bamigbola da Dr. Ibrahim Aminullahi-Ogunrinde sun yi zama sun saurari shari’ar rikicin aure guda biyu.

Kamin nan a jihohin Lagos, Ogun, Oyo and Osun ma an samu ,aman kotun shari’ar Musuluncin.

Zuwa yanzu, Jihar Ondo ce kadai bata da kotun shari’ar Musulunci a cikinta, hakanan itama Gwamnatin jihar Ekiti ta musanta cewa akwai kotun shari’ar musulunci a cikinta.

Tuni dai aka samu wani Fasto me suna Pastor Oluwafemi J. Edafemi, ya jagoranci gamayyar wasu masu ruwa da tsaki a yankin na Yarbawa inda suka yi gangamin cewa basu yadda da kotunan shari’ar Musulunci a jihohin nasu ba.

Karanta Wannan  ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *