Saturday, May 31
Shadow

Yau juma’a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da Sarki Sanusi II da Sarki Aminu Ado kowa ya naɗa nasa Galadiman

Yau juma’a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da masu ikirarin sarautar Kano biyu kowa ya naɗa nasa Galadiman.

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya jagoranci majalisarsa da hakimai da magoya bayansa naɗa ɗan uwansa Sunusi Ado Bayero, a matsayin sabon Galadiman Kano.

Shima Sarkin Kano Muhammad Sunusi ll ja jagoranci tasa majalisar da hakiman da ke masa biyayya da masoya in da ya naɗa ɗan uwan mahaifinsa wato Munir Sunusi, a matsayin sabon Galadiman Kano.

Sarautar Galadiman Kano ta rabu biyu ne tun bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya halarci fadar masarautar Kano da ke Kofar Kudu in da aka Sarki Sunusi ya yi nasa naɗin, yayin da magoya bayan jam’iyyar APC da ke adawa da Gwamnatin Kano su ka halarci fadar masarautar Kano da ke Nasarawa don sheda yadda Sarki Aminu ya gudanar da naɗinsa

Karanta Wannan  Wahala ta yi yawa, A tausayawa Talakawa>>Tsohon Shugaban kasa,Abdulsalam Abubakar ya roki Gwammati

Wa za ku ɗauka a matsayin Galadiman Kano?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *