
Rahotanni sun bayyana cewa, yawan wanda suka kasa biyan bashin da suka ci a bankunan Najeriya sun karu.
Yawan bashin da aka kasa biyan bankunan ya kai maki 7 cikin 100 wanda a baya maki 5 ne cikin 100.
Hakan na zuwane bayan da babban bankin Najeriya,CBN ya janye tallafin kan bashin da ya ke baiwa bankunan Najeriya.