
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle zai tafi kasar Egypt dan halartar taro kan tsaro da ake gudanarwa.
Taron za’a yishi ne tsakanin ranar 1 zuwa 4 ga watan Disamba a birnin Cairo na kasar ta Egypt.
Taron yakan hada batun tsaro na Afrika da gabas ta tsakiya.
Hakan na zuwane bayan da kiraye-Kiraye suka yi yawa akan a sauke karamin Ministan bayan da babban Ministan, Muhammadu Abubakar Badaru ya sauka daga mukaminsa.