Wednesday, January 15
Shadow

Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin kasar, duk kuwa da kara wahalhalun da ake fuskanta da ke janyo fushin jama’a.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na jiya a yayin bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya.

“Na fahimci matsalolin tattalin arziki da muke fuskanta a matsayinmu na kasa. Tattalin arzikinmu yana cikin tsananin bukatar gyara shekaru da yawa. Ba a daidaita shi ba saboda an gina shi a kan kura-kurai na dogaro da kudaden shigar da ake samu daga hako man fetur,” inji Tinubu.

Tun bayan hawansa ƙaragar mulki a bara, Tinubu ya cire da tallafin man fetur wanda ya haddasa tashin gwauron zabin sufuri da farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi a fadin kasar.

Karanta Wannan  Bama tunanin hadewa da kowace jam'iyya>>PDP

Dubban ‘yan Najeriya ne suka fito kan titunan Abuja da Legas a jiya Labara domin nuna adawa da yunwa da matsin tattalin arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *