Sunday, December 14
Shadow

Za a samar da ƙarin kayan aiki don daƙile ƴan ta da ƙayar-baya – Janar Chris Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa sojoji na aiki tukuru domin shawo kan matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a baya-bayan nan.

Ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin samar da ƙarin kayan aiki – musamman na sama domin ƙarfafa yaƙi da ƴan ta da ƙayar baya da ake yi.

Janar Musa ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da shugaban Najeriyar ya yi da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a.

Babban hafsan ya ƙara da cewa tuni aka sayo kayan yaƙin domin daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka zafafa kai hare-hare a ƴan watannin nan, musammman a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Karanta Wannan  Za'a kori Peter Obi daga jam'iyyar Labour Party saboda ya shiga hadakar 'yan Adawa ta kayar da Tinubu

“Shugaban ƙasa ya ba da umarnin abu na gaba da za a yi, da kuma haɗa-kai da sauran ƙasashe da muke makwabtaka da su saboda yanayin wurarensu ne ke ƙara rura wutar wannan lamari a ƙasar mu” in ji Janar Musa.

Ya ce an ƙara ƙarfafa rundunoni tare da sayan makamai domin ganin an magance wannan matsalar da aka daɗe ana fama da ita.

“Shugaban ƙasa na kuma duba yiwuwar tattaunawa da gwamnoni domin samun goyon bayansu ta hanyar tabbatar da cewa al’umma sun mori ribar dimokraɗiyya da kuma kakkaɓe ayyukan ƴan ta’adda,” in ji shi.

Babban hafsan tsaron ya alaƙanta ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya da ƙara ƙaimi da ƴan ta’dda da kuma masu ikirarin jihadi ke yi a faɗin yankin Sahel, inda ya ce abin da ya sa ƙasar ke cikin matsin lamba shi ne rashin kyawun yanayin iyakokinta.

Karanta Wannan  Nazir Sarkin Waka tare da Sheikh Dr. Mansir Yallawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *