
Wata mata dake zaune a gidan haya ta fasawa me gida kai bayan da ya bata notice ta tashi daga gidansa.
Me gidan wanda matashine kuma marayane ya bukaci matar ta tashi.
Lamarin ya farune a garin Umugbabe Ovoko dake karamar hukumar Igbo-Eze ta jihar Enugu.
Wani dan jarida daga jihar ne me suna, Chijinkem Ugwuanyi ya bayyana hakan inda yace tuni jami’an ‘yansansa sun kama matar da ‘ya’yanta 2.