
Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa a zaben shekarar 2027 zata doke Jam’iyyun APC da PDP.
Shugaban Jam’iyyar, Dr. Ajuki Ahmad ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Abuja inda yace zasu yi nasarar hakanne ta hanyar jagoransu, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso wanda shine zai zama shugaban kasar Najeriya a 2027
Duk da rikicin cikin gida da ya mamaye Jam’iyyar ta NNPP, Dr. Ajuki Ahmad yace a yanzu sun samu zaman lafiya a cikin Jam’iyyar.
Yace duk da yake hakan ba abune me sauki ba amma sun sha Alwashin cimma burinsu inda yace zasu fitar da Najeriya daga halin data tsinci kanta a ciki.