Friday, July 17
Shadow

Zamu fara amfani da Tattalin Arzikin Halal wanda kayan amfanin da Addinin Musulunci kadai ya yadda ayi kasuwancinsu zamu rika cinikinsu>>Inji Gwamnatin Shugaba Tinubu

Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, zata fara amfani da tattalin arziki na halal, wanda a Turance ake cewa Halal Economy

Wannan tattalin arziki ana kasuwancin kayan amfanin da addinin musulunci kadai ya yadda ayi amfani dasu ne, misali idan aka zo wajan nama, ba za’a yi kasuwancin Naman Alade ba da sauransu.

Mataimakin shugaban ma’ikatan fadar shugaban kasa, Senator Ibrahim Hassan Hadejia ne ya bayyanawa manema labarai na Thisday haka.

Yace kasancewar Najeriya na amfani da irin wadannan kaya suka ga cewa ya kamata suma su shiga harkar wannan tattalin arziki da ake yayi suma ayi dasu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wata 'yar kasuwa ta fashe da kuka bayan da ta aikawa kawarta Naira Miliyan 6 ta sayo mata jakunkuna daga kasar China amma ta aiko mata kwali ba komai a ciki

Yace kuma kar wani yayi tunanin wai saboda addini ne, yace Halal Economy ya na kusa da kaiwa darajar Dala Tiriliyan 7.

Yace kuma a cikin kasashen da suke amfani dashi, kasar Turkiyya ce kadai kasar Musulunci, sauran kasashen sune New Zealand, Australia, United States, Brazil da zauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *