
Jam’iyyar ADC ta caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen waje.
Jam’iyyar ta bayyana hakane ta bakin kakakinta, Bola Abdullahi inda yace ana kashe kudaden Talakawa wajan tafiye-tafiyen shugaban kasar.
Ya bayyana cewa, wannan shine karo 40 da shugaba Tinubu zai bar Najeriya tun bayan hawansa mulki kuma ya kwashe kwanaki 181 a kasashen waje.
Sanarwar tace wannan kusan watanni 6 kenan da shugaba Tinubu ya kwashe a kasashen wajan.
ADC tace tana Allah wadai da irin wadannan tafiye-tafiyen na shugaban kasa musamman ganin cewa babu wani abin ci gaba da hakan ya kawowa kasarnan.