Sunday, March 23
Shadow

Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio

Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, wato Arewa Consultative Forum ko kuma ACF a taƙaice ta nuna damuwarta kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi wanda kakakin ƙungiyar, Muhammad-Baba ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce akwai buƙatar a gudanar da bincike mai kyau domin tantance sahihancin zargin, kamar yadda tashar Channels a shafinta na intanet.

“A yanzu dai yadda abubuwa suke shi ne zargin nan zai iya ɓata sunan Najeriya a idon duniya,” in ji ƙungiyar, wadda ta nuna damuwa kan yadda a cewarta har zuwa yanzu, sanatocin arewa ne kaɗai suka fuskanci takunkumi kamar dakatarwa a majalisar ta 10.

Karanta Wannan  An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

“Wannan ya sa ACF ke fargabar ko dai abin ɓoye ne ya fara fitowa fili na yaƙi da yankin arewa. Wannan ya sa muke kira da a kawo ƙarshen wannan lamarin.”

Ƙungiyar ta yi kira da sanatocin arewa su goyi bayan Natasha, sannan ta buƙaci a gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *