Monday, July 27
Shadow

Ƴànbìndìgà sun kashe mutum 11 a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, na cewa kimanin mutum 11 wasu ‘yan bindiga suka kashe a garuruwan Zamfarawa da Dogon Hayi da kuma Ɗan Kurmi.

Harin ya zo ne mako ɗaya bayan da ƴanbindigar suka karɓi harajin da ya kai naira miliyan 60, wanda suka tilastawa dagatai tattara waɗannan kuɗi daga wajen jama’a.

Sai dai, duk da haka sun ci gaba da kai wa mutanen hare-hare.

Jihar ta Zamfara dai ta sha fama da hare-haren ƴanbindiga waɗanda ke garkuwa domin neman kuɗin fansa.

Duk da irin ƙoƙari da gwamnati ke cewa tana yi na daƙile ayyukansu – hakan ya citura saboda yadda suke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo:Jama'ar Katsina ku yi Hakuri, kamin in hau mulki na yi Alkawarin duk wata zan rika bada bayanin yawan kudaden da muka samu da yawan wanda muka kashe, amma yanzu da na zama Gwamnan naga abin ba zai yiyu ba>>Inji Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *