Friday, January 16
Shadow

Ƴan canji a Abuja sun dakatar da ayyuka don tantance masu sana’ar

Haɗakar ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta Abuja ta dakatar da ayyukanta domin tantance ma’aikatanta.

Shugaban ƙungiyar Alhaji Salisu Umar ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne domin tsaftace kasuwar.

Ya ce dama sukan yi haka lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ingancin sana’ar tasu.

Wakiliyar BBC da ta ziyarci kasuwar da ke unguwar Zone 4 a tsakiyar birnin Abuja, ta ce duka shaguna manya da ƙanana a kasuwar sun kasance a rufe.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ce Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya koma jihar Kebbi da zama har sai an kubutar da dalibai 'yan mata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *