Ƴan Sa Kai 11 Sun Rasa Rayukansu a Sokoto Bayan Artabu da Ƴan Bindiga
Aƙalla ‘yan sa-kai 11 ne aka tabbatar sun mutu, wasu da dama kuma ba’a san inda suke ba, bayan wani mummunan artabu da suka yi da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Tangaza da ke Jihar Sokoto.
Rikicin ya fara ne tun ranar Juma’a, inda aka samu rahoton mutuwar mutane biyu, amma daga bisani aka ƙara gano gawawwaki tara a dajin Lakurawa. Har yanzu ana ci gaba da neman wasu da ba a san inda suke ba, tare da taimakon sojoji da jami’an tsaro daga Binji da Racca.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan da ‘yan sa-kai suka hana wani hari a kauyen Magonho, lamarin da ya janyo musayar wuta mai tsanani.
Ƴan bindigar, wadanda yawansu ya kai 40, sun zo ne akan babura guda 20 dauke da manyan makamai. Sun kwashi dabbobi daga kauyen kafin su tsere.
Sojoji daga sansanin FOB da ke Masallaci sun bi su da gaggawa, inda suka kwato wasu daga cikin dabbobin da aka sace. Sai dai bayan wani lokaci, ‘yan bindigar sun sake dawowa kauyen Magonho, inda suka bude wuta tare da ƙona wata turken sadarwar MTN kafin su tsere.
Yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto domin gano sauran ‘yan sa-kai da aka rasa da kuma gano karin gawawwaki.