Akalla mutane 25 aka hallaka, sannan aka sace wasu da dama a lokacin da ƴanbindiga suka kai hari a wani ƙauyen a jihar Katsina a arewacin Najeriya, a cewar hukumomi.
Gwamman ƴanbindigar sun isa ƙauyen Yargoje da ke ƙaramar hukumar Ƙankara a ranar Lahadi da daddare ne, kamar yadda kwamishinan tsaro na jihar, Nasiru Babangida Mu’azu, ya shaida wa BBC Hausa.
Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun dinga harbin kan mai uwa da wabi, yayin da suka fasa shaguna tare da sace mutanen da kawo yanzu ba a san adadinsu ba.
Sai dai wasu rahotanni na cewa ƴanbindigar sun kashe fiye da mutane 50 tare da jikkata kimanin wasu 30.
A watan Disamba 2020, wasu ƴanbindiga sun sace ɗaliba 300 daga wata makarantar sakandare ta kwana ta maza da ke wajen Ƙankara, amma daga bisani aka sake su.
Matsalar ƴanfashin daji matsala ce da ta daɗe tana addabar jihar ta Katsina da wasu jihohin arewa-maso-yammacin ƙasar, duk da ƙoƙarin da hukumomi ke cewa suna yi domin magance matsalar.