Monday, June 2
Shadow

Ƴansanda na bincike kan mùtùwàr ƙananan yara biyar a cikin wata tsohuwar mota a Nasarawa

Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta ce ta fara bincike kan mutuwar wasu ƙananan yara biyar a garin Agyaragu cikin ƙaramar hukumar Obi a jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Ramhan Nansel, ya fitar yau Litinin a birnin Lafia.

Sanarwar ta ce an gano gawawwakin yaran ne a cikin lalatacciyar motar da ke ajiye a gidan wani Mista Abu Agyeme.

Ta ce tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, Shetima Jauro-Mohammed ya umarci gudanar da cikakken bincike don tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru.

A ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:30 na yamma ne, wani magidanci ya kai rahoto ga ‘yansanda cewa an gano ƙananan yara kwance shame-shame ba sa motsi a cikin wata lalatacciyar mota da ke yashe a harabar wani gida.

Karanta Wannan  Akwai haɗari kwanciya da waya a ƙarƙashin matashi-kai - Kwararre

Yaran waɗanda shekarunsu suka kama daga shida zuwa goma, mata uku ne sai maza biyu kuma an tabbatar da rasuwarsu ne a asibitin Aro da ke garin Agyaragu sakamakon abin da ake zargi shaƙewar numfashi ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *