Wednesday, May 21
Shadow

Ba matsala bane dan siyasar Najeriya ta koma Jam’iyya daya kawai, Adalcin Shugaba Tinubu ne yake kawo ‘yan siyasa APC>>Inji Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce samun jam’iyyu barkatai na dagula tafiyar da gwamnnati a tsarin dimokraɗiyya.

Abdullahi Ganduje ya shaida hakan ne bayan ganawa da Shugaba Tinubu tare da wasu ƴan majalisar PDP da suka koma APC.

Shugaban, ya ce idan duka jam’iyyun siyasar ƙasar za su narke su koma APC, suna maraba da hakan.

”Yanzu idan ka duba ƙasar China tsarin jam’iyya guda suke bi, amma yau ƙasar China jagora ce a duniya wajen samar da ci gaban al’ummarsu”.

Ganduje ya ce idan ƴan Najeriya suka buƙaci komawa tsarin jam’iyyar guda, ba wanda zai yi faɗa da hakan.

Ƴanmajalisar Dattawan Najeriya uku na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP daga jihar Kebbi za su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya tabbatar.

Karanta Wannan  Yawanci masu sharhi akan dakatar da sanata Natasha Akpoti jahilaine, kamar wanda ba musulmi bane yace zai fassara Qur'ani>>Sanata Godswill Akpabio

”Sanatocin jam’iyyar PDP daga jihar Kebbi a yau sun tabbatar wa shugaban ƙasa cewa sun fice daga jam’iyyarsu ta PDP tare da dawo jam’iyarmu ta APC”, in ji Ganduje.

Abdullahi Ganduje ya ce sanatocin uku za su bayyana wa majalisar dattawa matsayar tasu a mako mai zuwa kamar yadda kundin tsarin ƙasar ya tanadar.

Sanatocin Kebbi da suka sauya sheka.

Sanatocin uku sun haɗa da Sanata Adamu Aliero da Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi da kuma Sanata Garba Maidoki.

A baya-bayan nan batun sauya sheƙa tsakanin manyan ƴansiyasa na ci gaba da ɗaukar hankali a ƙasar, bayan da wasu jiga-jigan jam’iyun hamayya ke komawa APC mai mulki.

Ko a makonnin baya ma gwamnan jihar Delta da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa – wanda shi ne ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023 – suka sanar da komawa APC.

Karanta Wannan  Tsagin NNPP ya caccaki Kwankwaso bisa sukar waɗanda su ka bar jam'iyyar zuwa APC a Kano

‘Gaskiya ke halinta’

Sakataren jam’iyyar APC na kasa Malam Bala Ibrahim, ya ce gaskiya ce ke yin halinta.

A wata hira da BBC Malam Bala Ibrahim, ya ce, “Ga masu cewa muna fatan da matsaloli da rigingimu, ai yanzu suna jin kunya, kuma akwai wasu daga cikinsu ma har sun dawo jam’iyyarmu ta APC.”

“Wannan dai na ba wani abu bane face nuni da cewa manufofin jam’iyyar APC manufofi ne na gari wadanda suka zo dai-dai da dimokradiyya. Sanna ga adalci da tsari da ake bukata a dimokradiyya,” in ji shi.

Wasu da suka koma jam’iyyar APC daga jam’iyyun adawar sun ce rikice-rikicen da ake fama da su a jam;iyyarsu ne ya sanya su sauya sheka.

Karanta Wannan  ALLAHU AKBAR: An Yi Jana'izar Mutane 41 Da Sùķa Ŕaśù Sakamakon Hàďaŕìn Moțà A Hanyar Su Ta Zuwa Wajen Zagayen Mauĺùďì Daga Garin Kwandari Zuwa Samunaka

‘Rashin akida’

Sai dai kuma Umar Ibrahim Tsauri, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya shaida wa BBC cewa rashin akida ce ke sanya wasu sauya sheka.

Ya ce ” Mafi yawan mutanen da ke sauya sheka musamman a yanzu ba mamaki ko dai sun nemi wani abu a jam’iyyar da suke basu samu ba, ko kuma suna hangen cewa a adawa ba a samun komai gara su koma jam’iyya mai mulki.”

Sauya shekar ‘yan siyasa dai abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya.

Masana kimiyyar siyasa a Najeriya dai sun ce ‘yan siyasar kasar basu gaji azumin siyasa ba. Salon sauya shekar dai na tasiri wajen karawa jam’iyya mai mulki karfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *