Monday, June 2
Shadow

2027: Kuri’un Buhari miliyan 12 har yanzu na APC ne, inji Gwamna Sule

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari har yanzu yana da matukar muhimmanci ga jam’iyya mai mulki, wato APC, gabanin zaben 2027.

Gwamna Sule ya ce kuri’un Buhari da yake samu guda miliyan 12, za su ba jam’iyyar mai mulki rinjaye a zaben mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani babban taron girmamawa da aka gudanar domin Sakataren Gwamnatin Jihar, Barr. Labaran Magaji, a fadar gwamnati da ke Lafia, babban birnin jihar.

Sule ya soki wadanda ke ganin cewa Buhari da magoya bayansa za su bar hadin gwiwar da ta haifar da jam’iyyar APC, yana mai cewa Buhari har yanzu yana daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar kuma yana da tasiri wajen samun nasara a zaben da ke tafe.

Karanta Wannan  20 daga Yaran da Gwamnatin tarayya ke tsare dasu bisa tuhumar cin amanar kasa zun kwanta rashin lafiya

Ya kara da cewa duka Buhari da Shugaba Bola Tinubu sun dade suna aiki tare wajen kafa jam’iyyar APC, yana mai jaddada cewa hadin kai tsakaninsu yana kara karfi gabanin zaben 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *