
Wasu jami’an soji sun ce sun ƙwace cikakken iko da ƙasar Guinea-Bissau a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an kama shugaban ƙasar Umaro Sissoco Embaló.
Jim kaɗan bayan an ji ƙarar harbe-harbe a Bissau babban birnin ƙasar, majiyoyin gwamnati sun shaida wa BBC cewa an tsare Embaló.
Daga nan sai jami’an soji suka bayyana a gidan talabijin na ƙasar, inda suka ce sun dakatar da gudanar da zaɓen ƙasar da aka gudanar kuma za su ci gaba da tafiyar da harkokin ƙasar.
Al’ummar ƙasar ta yammacin Afirka na dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka hana dan takarar jam’iyyar adawa tsayawa takara.
A ranar Alhamis ne ake sa ran sakamakon kuma Embaló da abokin hamayyarsa Fernando Dias sun yi iƙirarin nasara.
Janar Denis N’Canha, shugaban sojoji na fadar shugaban ƙasa, ya karanta wata sanarwa da ta ayyana kwace mulki tare kuma da rufe iyakokin ƙasar.
Janar N’Canha ya umurci jama’ar ƙasar da su “kwantar da hankulansu”.
Baya ga Embaló, an kama hafsan sojojin shugaban ƙasa da wasu ministoci da dama.
Rahotanni sun ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya makale a kasar inda juyin mulkin ya rutsa dashi.