Saturday, March 15
Shadow

Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 36 wajan Tafiye-Tafiye a shekarar 2024

Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta a kashe Naira Biliyan 36.3 wajan tafiye-Tafiye a shekarar 2024 data gabata.

Kafar Open Treasury Portal ce ta bayyana hakan a wasu bayanai data tattara inda tace shugaban ya kashe kudadenne wajan tafiye-Tafiye zuwa kasashen waje.

Bayanan sunce idan aka hada da kudaden da shugaban kasar ya kashe a tafiye-Tafiyen da yayi na cikin gida, ya kashe jimullar Naira Biliyan 83 kenan.

Yawan kudaden da shugaban ke kashewa wajan tafiye-Tafiyen sun sakawa ‘yan Najeriya damuwa musamman ma lura da yanda gwamnati ke kukan karancin kudin gudanar da ayyuka.

Peter Obi a kwanakin baya yayi kira ga shugaba Tinubu da ya rage yawan tafiye-Tafiyen da yake yi.

Karanta Wannan  Cutar Zazzabin Lassa ta kkàshè mutane 10 a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *