
Rahotanni sun bayyana cewa, cutar zazzabin Lassa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 a Najeriya.
Lamarin ya farune a jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Benue, Gombe, Kogi, da Ebonyi.
A shekarar da muke ciki, cutar ta kashe jimullar mutane 80 a kananan jihohi 63 na jihohi 11.
Hukumar kula da lafiya ta kasa, NCDC ce ta bayyana hakan a sanarwar da take fitarwa ta mako-mako.