
Mahukunta a jihar Legas sun kama magidanci dan kimanin shekaru 38 da abokinsa da suka hadu sukawa agolarsa me shekaru 14 fyade.
Kakakin ‘yansandan jihar, CSP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar.
Ya kara da cewa, mahaifiyar yarinyarce ta kai koke a ofishin ‘yansanda dake yankin Okokomaiko na jihar.
Rahoton yace sun dirkawa yarinyar ciki inda a yanzu tana dauke da cikin wata 9.
Ya kara da cewa, da zarar an kammala bincike, za’a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.