Saturday, May 17
Shadow

Jam’iyyar PDP ta lashe gaba dayan zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Osun

Rahotanni daga zaben kananan hukumomin jihar Osun da ya gabata ya nuna cewa, Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben a kafatanin kananan hukumomin jihar.

Kwamishinan zabe na jihar, Hashim Abioye ne ya bayyana hakan bayan kammala zaben inda yace PDP ce ta yi nasara a kananan hukumomi 30 da mazabu 323 dake fadin jihar.

Yace an samu nasarar kammala zaben cikin nasa.

Yace Jam’iyyu 18 ne suka yi takara a zaben kuma PDP ce ta lashe zaben na kananan hukumomi dana kansiloli baki daya.

Karanta Wannan  Matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za'a ce mutane su fara tashi suna kare kansu ba>>Inji Gwamnan jihar Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *