
A wani abin mamaki da ya faru, an kama wasu dake sayar da kwaroron roba da ya lalace.
Suna canja masa mazubine da kuma shekarar da ya kamata ya lalace inda suke sake sayar dashi kamar sabo. Kuma shi wannan kwaroron roba, hukumar kasar Amurka, USAID ce ta bayar dashi kyauta.
Masana ilimin lafiya sun bayyana cewa, amfani da kwaroron roba da ya lalace zai iya sawa ya huje yayin da ake amfani dashi wanda hakan ka iya kaiwa ga daukar cikin da ba’a shirya ba da muna kamuwa da cutukan da ake dauka a wajan jima’i.
Tuni dai hukumomi a ma’aikatar lafiya suka sanar da daukar matakan fara binciken dan gano masu aikata irin wannan ta’asa.