Friday, December 5
Shadow

Ji yanda aka gano gawarwakin mutane 30 a Najeriya da aka yanke musu sassan jikinsu dan yin tsafi

A yankin Oriendu na jihar Abia, mutane na cikin fargaba da tashin hankali bayan da aka rika tsintar gawarwakin mutane musamman mata wadanda aka cire musu al’aura.

Lamarin ya fara faruwane tun daga shekarar data gabata.

Basaraken yankin, HRH Eze Philip Ajomiwe, ya tabbatarwa da jaridar Leadership hakan.

Yace ‘yan sa kai sun kasa magance matsalar saboda mahara da ame zargin matsafa ne na da muggan makamai.

yace dan haka suna kira da gwamnati data kai musu dauki.

Karanta Wannan  Wannan wane irin hukunci ne? Kotu ta daure barawon doya wadda kudinta bai wuce Naira 35,000 shekaru 3 a gidan yari, da aiki me wahala, sanan babu zabin biyan tara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *