
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa ‘a yanzu Uba Sani ba abokinsa ba ne’ bayan abubuwan da ke faruwa baya-bayan nan.
El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya gudanar da tashar talabijin ta Arise da yammacin yau Litinin.
Bayan kammala wa’adinsa na shekara takwas a matsayin gwamnan jihar Kaduna, tsohon gwamnan na fuskantar bincike kan kuɗaɗe da ake zargin sun yi ɓatan-dabo a lokacin mulkinsa.
Lamarin ya haifar da muhawara kasancewar thonon gwamnan na Kaduna, Nasir El-Rufa’i da gwamna mai ci Uba Sani sun kasance masu kusanci a tsawon shekara takwas na mulkin tsohon gwamnan.
El-Rufa’i ya bayyana cewa aboki shi ne mutumin da zai kawo maka ɗauki ko a lokacin daɗi ko na tsanani.
Ya ce “a yanzu Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne.
“Na san cewa abokaina sun san cewa zan iya kai musu ɗauki a kowane lokaci,” in ji tsohon gwamnan.
A game da zargin da ake yi masa, El-Rufa’i ya ce bai taɓa cin ko sisi na kuɗaden da ba nashi ba a muƙaman da ya riƙe.