
Rahotanni sun bayyana cewa, dalibin jami’ar Federal University, Otuoke jihar Bayelsa ya nutse a ruwa bayan da suka yi caca shi da abokansa.
Dalibin sun yi gaddama da abokansa kan cewa, ba zai iya tsallake wani ruwa bane da iyo inda shi kuma yace zai iya.
Anan ne sai suka saka Naira Dari uku kowannensu shi da abokansa.
Ya shiga ya fara iyo a cikin ruwan sai suka ga ya nutse, har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba’a gano gawarsa ba.
Rahoton jaridar Punchng ya bayyana cewa an yi kokarin tuntubar hukumar makarantar dan jin ta bakin kakakin makarantar Ms Mercy Ekott, saidai an ta kiran wayarta amma taki dagawa.
An kuma tuntubu kakakin ‘yansandan jihar, Mr Musa Mohammed inda yace bai san da maganar ba.