Saturday, December 13
Shadow

Da Duminsa: ‘Yan Bìndìgà sun tare ‘yansandan Najeriya sun kashe 2 daga ciki

Tawagar ‘yansandan Najeriya da suka fita aiki a karamar hukumar Jos dake jihar Filato sun gamu da kwantan baunar ‘yan Bindiga inda suka afka musu suka kashe ‘yansanda 2.

Lamarin ya farune akan titin Little Rayfield Road da misalin karfe 7:30 pm.

Ana zargin dai ko ‘yan Fashi ko masu garkuwa da mutanene suka afkawa ‘yansandan.

‘yansandan da aka kashe sune Inspector Fatoye Femi da Inspector Dafur Dashit.

An kama daya daga cikin maharan me suna Auwal Ali.

Karanta Wannan  Na rasa wace irin matace Sanata Natasha Akpoti, ta kawo mana korafi, ba'a gama bincike ba ta tsallaka ta kai kara kotu, ba'a gama shari'a ba ta sake tsallakewa ta kai korafi majalisar Dinkin Duniya>>Sanata Godswill Akpabio

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *