
Tawagar ‘yansandan Najeriya da suka fita aiki a karamar hukumar Jos dake jihar Filato sun gamu da kwantan baunar ‘yan Bindiga inda suka afka musu suka kashe ‘yansanda 2.
Lamarin ya farune akan titin Little Rayfield Road da misalin karfe 7:30 pm.
Ana zargin dai ko ‘yan Fashi ko masu garkuwa da mutanene suka afkawa ‘yansandan.
‘yansandan da aka kashe sune Inspector Fatoye Femi da Inspector Dafur Dashit.
An kama daya daga cikin maharan me suna Auwal Ali.