
Sanata me wakiltar Birnin Tarayya, Ireti Kingibe ta bayyana cewa dama can sanata Natasha Akpoti da kakakin majalisar, Godswill Akpabio sun san juna kuma akwai wani abu a tsakaninsu kamin ta zama sanata.
Ta bayyana hakane a yayin da sanata Natasha Akpoti ta fito ta zargi kakakin majalisar da cewa ya nemeta da lalata ne ta ki shiyasa ya canja mata gurin zama a majalisar kuma yake dakile kudirorin da take kawowa.
Sanata Ireti Kingibe ta bayyana cewa, ba Sanata Natasha Akpoti kadai bace aka canjawa wajan zama a ranar ba.
Ta jawo hankalin cewa hakan tsari ne na majalisar wanda kuma duk dan majalisar ya kamata yana girmama hakan.