
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin majalisar dattijai da cewa ya kamata au binciki kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio kan zargin da Sanata Natasha Akpoti tai masa na son yin lalata da ita.
Atiku a sanarwar da ya fitar ya nemi cewa a matsayin Akpabio na mutum na 3 wanda yafi karfin fada aji a Najeriya, ya kamata ace yana da mutunci da tsare kai da tarbiyya.
Atiku yace ya kamata a kafa kwamiti na musamman me zaman kansa da zai binciki sanata Akpabio kan wannan zargi.
Atiku yace wannan lamari zai sa Duniya ta fahimci irin tsarin Adalci da Najeriya ke da shi.