Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun gargaɗi ƴan Najeriya kan sake zaɓen APC a 2023.
Tsohon gwamnan na Sokoto ya bayyana cewa halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan yanzu, kin ɗaukar shawara ne ya kawo shi.
Tambuwal ya bayyana hakane a wajan wani taron maau ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Sokoto.
Yace sun gayawa mutane, APC mulki kawai take aon samu ta ganta a ofis.
Yace gashi yanzu sun samu amma sun rasa yanda zasu yi dashi.