Saturday, March 15
Shadow

Hukumar EFCC tace itace ta kai samame Otal a Jihar Naija ba ‘yan Bìndìgà ba

A jiyane dai muka samu rahoton cewa, ‘yan Bindiga cikin shiga irin ta EFCC sun kai samame wani otal dake Chanchanga inda suka sace mutane 10.

Saidai a yau, hukumar EFCC ta fito inda ta bayyana cewa, itace ta kai wannan samame ba ‘yan Bindiga ba.

Hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa, ta samu bayanai akan wasu ‘yan damfarar yanar gizo ne dake zaune a otal din inda wakilanta na jihar Kaduna suka kai samame kan otal din me suna WhiteHill Hotel dake Chanchaga a jihar ta Naija.

Sanarwar tace an kama mutane 11 daga otal din sannan hukumar tace ta gudanar da aikinta cikin kwarewa da bin doka dan haka bata san daga inda maganar ‘yan Bindiga ta samo asali ba.

Karanta Wannan  Na samu karin Lafiya sosai bayan dana sauka daga Mulkin Najeriya>>Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Hakanan kuma sanarwar tace an kwace motoci 2 da wayoyin hannu 13.

Sanarwar tace za’a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike game dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *