Saturday, May 17
Shadow

Wasu bala’o’i sun aukawa kasar Amurka inda A birnin Los Angeles aka yi girgizar kasa, a South Carolina gobarar daji ce ta kunno kai

An samu girgizar kasa me maki 3.9 a birnin Los Angeles na Jihar California ta kasar Amurka.

Hakan na zuwane bayan da aka kammala bikin bayar da kyautar Oscar 2025.

Gurare da yawa da suka hada da Pasadena, Long Beach, San Fernando Valley, Torrance, Redondo Beach da Glendale sun bayyana cewa sun ji motsin kasa.

Babu dai rahoton cewa wani ya ji rauni.

Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da aka samu mummunar gobarar daji a birnin na Los Angeles.

Hakanan a jihohin South Carolina da North Carolina na kasar Amurkar ma Wutar daji ce ta barke inda ake maganar taci kadada sama da 1,600 a South Carolina inda a North Carolina kuma taci kadada sama da 500.

Karanta Wannan  Ina Nan A Raye Amma Ba A Kulle Nake Ba, Batun Kamu Kuma A Koda Yaushe Za A Iya Kama Ni, Kuma A Shirye Nake Koda Zan Ŕàsà Raiña, Tunda Dama Sùn Jimà Suña Ñemañ Rabà Nì Da Rayùwațà, Kuma Ina Godiya Da Addù'o'inku Masoyana, Inji Odinari Ahmed Isa

Mahukunta a yankunan da gobarar ta tashi sun bayar da umarnin mutane su fice daga yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *