
Bankin (Afreximbank) ya bayyana cewa, Najeriya ce kasa ta 3 a jerin kasashen da suka fi yawan cin bashi a Africa.
A wani bayani da ya fitar, bankin yace yawan ciyo bashi daga kasashen waje a tsakanin kasashen Adrica na ci gaba da karuwa.
Yace hakan na faruwane saboda rashin ci gaban bangaren hada-hadar kudi na kasashen Afrikan.
Bankin yace a watanni 6 na farkon shekarar 2024, kasashen Afrika 10 ne ke da kaso 69 na yawan bashin da aka ciwo a nahiyar.
Kasashen sune South Africa (14%), Egypt (13%), Nigeria (8%), Morocco (6%), Mozambique (6%), Angola (5%), Kenya (4%), Ghana (4%), Côte d’Ivoire (3%), sai Senegal (3%).
Bankin yace hakan na kara karuwane saboda yawan dogaron da kasashen ke yi da samun kudi ta hanyar neman tallafi daga kasashen yamma.