
Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaddamar ta tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman a faɗin jihar.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta ftitar, ta ce tallafin – wanda ya ƙunshi rabon kuɗi – zai shafi masu buƙata ta musamman duka ƙananan hukumomin jihar.
Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce tallafin zai shafi cibiyoyi 27 na masu buƙata ta musamman a fadin jihar.
Gwamnan kuma yi kira ga waɗanda za su amfana da tallafin su bayar da haɗin kai domin kauce wa turmutsitsi a wajen raba tallafin