Monday, May 19
Shadow

Mai magana da yawun tsofaffin shugabannin Nijeriya Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, Dr. Doyin Okupe ya mutu yana da shekaru 72 a duniya.

An sanar da mutuwar fitaccen ɗan siyasa Adedoyin Ajibike Okupe (22 ga watan Maris 1952 – 7 ga watan Maris 2025), wanda aka fi sani da Dr. Doyin Okupe da safiyar Juma’a.

Okupe likita ne kuma ɗan siyasa wanda ya kafa cibiyar kula da lafiya ta Royal Cross kuma ya kasance sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar National Republican Convention (NRC).

An taba tsare shi a ƙarƙashin mulkin marigayi Janar Sani Abacha, kuma daga baya aka hana shi shiga takarar fid da gwani a jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP). Daga baya, ya kasance ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Ogun.

Okupe ya kasance mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai a gwamnatin Olusegun Obasanjo da kuma babban mataimaki na musamman kan harkokin jama’a ga Goodluck Jonathan.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Kamar yanda yayi da Amarya, A'isha Humaira, Rarara kuma ya dauki hotuna da Uwargidansa

Ya mutu ya bar mata ɗaya da ƴaƴansu biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *