
Hukumar kididdiga ta kasa, NBS tace Najeriya ta samu kudin ahiga da suka kai Naira Tiriliyan 13.78 daga sayar da danyen man fetur a watanni 3 na karshen shekarar 2024 data gabata.
A sanarwar da suka fitar sun ce Najeriya ta kuma samu kudin shiga daga harkokin da ba na man fetur ba da suka kai Naira Tiriliyan 2.8 da kuma Naira Tiriliyan 6.2.
!Hakanan hukumar tace har yanzu dai abinda Najeriya ta fi fitarwa dan sayarwa da samun kudin shiga daga kasashen Duniya danyen man fetur ne wanda ke wakiltar kaso 68.87 cikin 100 na kudin shigar gwamnatin.