
Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Akwai mata da yawa kyawawa da yayi aiki dasu amma babu wadda ta taba zarginsa da neman yin lalata da ita sai Sanata Natasha Akpoti.
Ya bayyana hakane a wajan taron ranar mata ta Duniya.
Sanata Akpabio yace zargin da Sanata Natasha Akpoti ta yi masa ya girgiza Majalisar inda yace abin ya basu mamaki.
Yace amma dadin abin bashi kadai ne ta taba yiwa irin wannan sharri ba da kuma ta kasa kawo shaida.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ma ya zargi Sanata Natasha Akpoti da cewa shima ta taba kala masa sharrin yin lalata da ita amma daga baya aka gano karyane.