Friday, July 17
Shadow

Da Duminsa:Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za’a yi zaben shugaban kasa na shekarar 2027

Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta sanar da ranar 20 ga watan Fabrairu na shekarar 2027 a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Shugaban Hukumar zaben, Professor Joash Amupitan ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

Yace zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisun tarayya za’a yishi ne ranar 20 ga watan Fabrairu inda kuma zaben Gwamnoni dana ‘yan majalisar jihohi za’a yishi ne ranar 6 ga watan Maris.

Ya bayyana cewa, sun shirya tsaf dan gudanar da zaben.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Shugaba Bola Ahmed ya isa birnin Tokyo na kasar Japan Gabannin taron TICAD na 2025, Ambasada Hideo MATSUBARA, jakadan Japan mai kula da TICAD ya tarbe shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *