
‘ya’yan Marigayi Janar Sani Abacha sun gargadi tsohon shugaban kasar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB cewa ya daina batawa mahaifinsu suna.
Sanarwar wadda daya daga cikin ‘ya’yan Sani Abachan, Muhammad Abacha ya fitar tace IBB ya zargi cewa Abacha da cewa shine yayi sanadiyyar soke zaben zaben Abiola.
Saidai sanarwar tace wannan ikirari na IBB ba gaskiya bane, duk da yake cewa, Abacha babba ne a gwamnatin IBB din amma IBB din shine shugaban kasa.
A karshe dai sun gargadi IBB din da ya daina batawa babbansu suna.