Saturday, March 15
Shadow

Ku kiyayi kanku da tunanin fita kasar waje ci rani, da yawa da suka je suna cikin nadama>>Gwamnati ta gargadi Matasa

Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen Ketare, Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa da yawan ‘yan Najeriya da suka je kasar waje ci rani suna cikin halin nadama da dana sani.

Ta bayyana hakane ta kafar X inda tace da yawan ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen na ketare na damun ta da maganar cewa suna cikin nadama da dana sanin fitar da suka yi.

Ta mayar da martanine akan ikirarin wani lauya dan Najeriya dake zaune a kasar Ingila inda yake cewa lamarin cirani a kasar ta Ingila ya canja inda da yawa suke cikin nadama da damuwa da danasani.

Yace kamin mutum ya sayar da kadararsa ya tafi kasar Ingila ci rani yayi tunani kada kawai dan ya ga wani yayi shima yace zai yi.

Karanta Wannan  Da Duminsa: 'Yan Bìndìgà sun tare 'yansandan Najeriya sun kashe 2 daga ciki

Yace idan mutum na da aikinsa me kyau, ya rike abinsa kada yace sai ya je ingila.

Tace inda ake tafiya ci ranin, yafi Najeriya muni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *