
Shugaban kwamitin da’a na majalisar dattijai Sanata Neda Imasuen wanda shine ya bayar da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti tsawon watanni 6, shi kuma kasar Amurka ta hanashi shiga kasarta saboda zargin rashawa da cin hanci.
Yana da kamfanin aikin Lauya, kuma wata mata ta kawo masa aikin ya wakilceta a kotu, saidai maimakon ya wakilceta, bayan da ta biyashi kudin aiki, sai ya tsere da kudin ba tare da ya je ya wakilceta a kotun ba.
Hakanan rahoton yace an nemi a bincikeshi amma yaki.
Matar me suna Daphne Shyfield a shekarar 2009 ta baiwa Sanata Neda makudan kudade ya wakilceta a kotu amma ya tsere da kudinta kuma yaki wakiltarta a Kotu.