
Majalisar mata ta majalisar Dinkin Duniya ta bayyanawa Sanata Natasha Akpoti cewa, ta ji zargin da takewa kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio sannan zata so ji daga bakin sanata Godswill Akpabio din da majalisar dattijai ta Najeriya kamin sanin matakin da ya kamata ta dauka.
Kakakin majalisar, Tulia Ackson ce ta gayawa Sanata Natasha Akpoti haka bayan da ta gama bayyana korafinta.
Ta cewa sanata Natasha Akpoti maganar da ta yi bata cikin abinda ya tarasu a majalisar amma duk da haka zasu ji daga bakin majalisar dattijai ta Najeriya da kuma wanda ake zargi, Sanata Godswill Akpabio kamin su dauki mataki.
A jiya ne dai Sanata Natasha Akpoti ta kai kakakin majalisar kara a gaban kwamitin mata na majalisar Dinkin Duniya.